Wasu kannen miji sun kashe matar yayansu saboda ta zagi mahaifiyar su
- Wata mata mai suna Hadiza Salisu ta rasa ranta bayan da kannen mijinta su ka yi mata bugun dawa saboda ta zagi mahaifiyar su
- Malam Salisu Dan Kasuwa, mahaifin Marigayiya Hadiza, ya ce, 'yar ta sa ta sha yin yaji daga gidan mijin saboda tsangwamar da surukar ke yi mata
- Hukumar 'yan sanda a jihar Katsina, ta bakin kakakinta, Gambo Isa, ta tabbatar da faruwar al'amarin
Wata mata mai suna Hadiza Salisu ta rasa ranta bayan da wasu kartin samari, kannen mijinta, su ka yi mata bugun dawa saboda ta zagi mahaifiyar su.
Wannan abin takaici ya faru ne a garin a garin Layin Mahuta dake karkashin karkashin karamar hukumar Dan Ja a jihar Katsina.
Dama dai an ce ba'a ga maciji tsakanin Hadiza da mahaifiyar mijinta, surukar ta, saboda yadda mahaifiyar mijin ke zargin yana fifita matar a kanta.
Malam Salisu Dan Kasuwa, mahaifin Marigayiya Hadiza, ya ce, 'yar ta sa ta sha yin yaji daga gidan mijin saboda tsangwamar da surukar ke yi mata, musamman ganin cewar mijin Hadiza ba mazauni bane.
DUBA WANNAN: Balahirar kisan da amarya ta yiwa angon ta a Katsina: Ta kashe shi ne domin boye wani abin kunya
Da yake shaidawa gidan jaridar BBC, Dan Kasuwa ya ce "ko a ranar da kannen mjin Hadiza su ka kashe ta saida Maigari ya yi masu sulhu, amma duk da haka su ka bi dare su ka yi mata bugun dawa da itatuwa har ta kai da zubar jini ta yi sanadiyar mutuwar ta."
Hukumar 'yan sanda a jihar Katsina, ta bakin kakakinta, Gambo Isa, ta tabbatar da faruwar al'amarin. Kazalika hukumar ta ce tuni ta damke kannen mijin da suka aikata wannan aika-aika kuma tana gudanar da bincike a kansu a hedikwatar hukumar dake Katsina. Hukumar ta ce da zara ta kammala bincike za ta gurfanar da su gaban kotu domin girbar abinda suka shuka.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng