Yanzu Yanzu: Evans, biloniyan dake garkuwa da mutane ya kai karan yan sanda kan kwace masa manyan motocin daukar kaya 25

Yanzu Yanzu: Evans, biloniyan dake garkuwa da mutane ya kai karan yan sanda kan kwace masa manyan motocin daukar kaya 25

Shahararren biloniyan nan dake garkuwa da mutane, Chukwudumeme Onwuamadike wanda aka fi sani da Evans ya sake maka yan sanda a kotu, inda ya bukaci a saki manyan motocin daukar kayansa kirar Mack guda 25 da aka kwace a hannunsa.

Lauyansa, Olukoya Ogungbeje, ya yi jayayya a daukaka karan cewa an kwace manyan motocin daukar kayan ne ba tare da wani umurni daga kotu ba, cewa kwace kadarorin ya saba ma yancin Evans.

Ogungbeje na rokon babban kotun tarayyan dake Lagas da ta umurci yan sandan da su saki motocin ga Evans ta hannun shi (Ogungbeje).

Yanzu Yanzu: Evans, biloniyan dake garkuwa da mutane ya kai karan yan sanda kan kwace masa manyan motocin daukar kaya 25
Yanzu Yanzu: Evans, biloniyan dake garkuwa da mutane ya kai karan yan sanda kan kwace masa manyan motocin daukar kaya 25

Ya lissafa lambar wasu daga cikin motocin a matsayin BDG 78 XT, GGE 491 XU, FST 742 XT, AGL 219 XT, BDG 79 XT, AGL 222 XT, GGE 492 XU, AGL 220 XT da kuma GGE 489 XU.

KU KARANTA KUMA: Shugaban kasa Buhari ya gana da shugabannin tsaro a fadar shugaban kasa

A cewarsa, yan sandan sun kwace motocin daga hannun Evans ta karfin tuwo a ranar 15 ga watan Yunin 2017 ba tare da umurnin kotu ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng