Rundunar mayaƙan Sojan ƙasa ta ƙaddamar da sabon aiki na musamman don yaki da barayin mutane

Rundunar mayaƙan Sojan ƙasa ta ƙaddamar da sabon aiki na musamman don yaki da barayin mutane

A kokarinta na karkare yaki da masu garkuwa da mutane da suka addabi jihar Kaduna da Neja, rundunar Sojan Najeriya ta kaddamar da wani sabon aiki na musamman, mai taken ‘Karamin goro’, inji rahoton Daily Trust.

Mataimakin Kaakakin rundunar Soji, kanal Muhammad Dole ya sanar da haka a ranar Alhamis 25 ga watan Janairu, inda yace rundunar ta kaddamar da wannan aiki ne don magance sauran tsirarun barayin mutanen da suka rage a dajin Birnin Gwari, da hanyar Sarkin pawa.

KU KARANTA: Wani Saurayi ya dirka ma budurwarsa ciki, kuma ya kashe mahaifinta

“Sakamako cigaba da ayyukan masu garkuwa da mutane, rundunar Sojin Najeriya ta kaddamar da sabon aiki na musamman don yakar barayin tare da fatattakar su daga sansanoninsu, don tsaron dukiya da rayukan jama’an dake bin hanyar

Rundunar mayaƙan Sojan ƙasa sun ƙaddamar da sabon aiki na musamman don yaki da barayin mutane
Rundunar mayaƙan Sojan ƙasa

“Rundunar sojan kasa za ta samu hadin gwiwar rundunar Sojan sama, wanda za su yi amfani da jiragensu wajen yi ma barayin luguden wuta, tare da goyon bayan rundunar tsaro ta sirri, DSS, da kuma rundunar tsaro ta farin kaya, NSCDC.” Inji sanarwar

Kaakakin ya cigaba da bayyana dazukan dake yankin sun zama mafaka ga masu aikata munanan laifuka, wanda hakan ya sanya jama’an kauyuka da dama suka tsere daga garuruwansu don tsira da rayukansu, do haka ne ‘Operation Karamin goro’ ya zama wajibi don hana barayin sakat, tare da kawo karshen su.

Daga karshe shugaban rundunar sojan kasa ta daya, Manjo Janar Mohammed Mohammed ya nemi hadin gwiwar jama’a a yakin da suke yi da masu garkuwa da mutane, ta hanyar baiwa Sojoji bayanai da zasu taimaka musu a kokarin da suke yi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng