Ana siyar da wasikar da Obasanjo ya aika ga shugaba Buhari a Abuja
- Wasu yan Najeriya sun fara samun alfanu daga wasikar da tsohon shugaban kasa Obasanjo ya aika zuwa ga shugaba Buhari
- An tattara wasikar waje daya sannan kuma ake siyar da shi a Abuja, babban birnin tarayyan Najeriya
- A cikin wasikar Obasanjo ya soki shugaban kasar kan wasu al’amuran kasar
Yan sa’o’I kadan bayan tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya saki wani dogon wasika mai zafi ga shugaban kasa Muhammadu Buhari akan halin da kasa ke ciki, wasu yan Najeriya sun tattara wasikar waje daya sannan suna siyarwa a Abuja.
A yanzu haka wasikar da tsohon shugaban kasar ya rubuta na ci gaba da haifar da cece-kuce a tsakanin yan Najeriya sannan kuma ana ganin hakan babban kalubale ne ga fadar shugaban kasa Buhari kamar yadda ake kallon Obasanjo a matsayin daya daga cikin manyan masu fada a ji a kasar, kuma ana ganin hakan zai shafi kudirinsu na 2019.
KU KARANTA KUMA: Ana ci gaba da yunkurin dakatar da Bukola Saraki
Legit.ng ta tuna cewa Obasanjo ya taba rubuta wasika makamancin haka ga gwamnatin tarayya lokacin mulkin Jonathan sannan kuma Jonathan ya ki bin shawarar tsohon shugaban kasar wanda hakan yayi sanadiyar faduwarsa a zaben 2015.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng