Waiwayen baya: Yadda Obasanjo ya janyo wa siyasar Jonathan cikas a 2013
- Buhari shine shugaba na hudu da Obasanjo ya rubutawa budadiyar wasika yana kalubalanatar yanayin shugaban cin sa
- Wasikar da Obasanjo ya rubutawa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a 2013 ya janyo ma siyasar sa cikas har ya fadi zabe a 2019
A ranar Tatala 23, ga watan Janairu,2018 tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya rubutawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari budadiyar wasika akan kada ya kara tsayawa takara.
Wannan wasika ya janyo cecekuce a cikin al’umman Najeriya musamman a shafukan sada zumunta.
Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose yayi kaca-kaca a Obasanjo akan wannan wasika da ya rubutawa shugaba Buhari inda yace rashin adalci da son kai yasa Obasanjo ya rubuta wasikar.
Tarihi ya nuna shugaban kasa Muhammadu Buhari shine shugaba na hudu dake kan mulki da Obasanjo ya rubutawa ma sa bududiyar wasika yana kalubalanatar yanayin shugabancin su.
A cikin shugabanin da Obasanjo ya rubutawa budaddiyar wasika a baya akwai, marigayi Janar Sani Abacha wanda ya daure Obasanjo a kurkuku, sai, Ernest Shonekan, wanda yayi kwanki 90 akan karagar mulki Najeriya sai Goodluck Jonathan.
KU KARANTA : Fayose yayi kaca-kaca da Obasanjo akan budaddiyar wasikar da ya rubutawa Buhari
A shekara 2013, tsohon shugaba kasar Najeriya, Cif Obasanjo ya rubutawa tsohon shugabankasa, Goodluck Jonathan, budadiyar wasika akan kada ya tsaya takara a zaben 2015.
A cikin wasikar Obasanjo ya nuna takaicinsa aka yadda a ya bar cin hanci da rashawa da satar kudin jama'a ta kowane hali suka zama abun kawa a kasar karkashin shugabancin Jonathan, musamman a harkokin gwamnati.
Haka ma wasikar ta bayyana takaicin tsohon shugaban kasar yadda jam'iyyar dake gwamnati ke marawa 'yan adawa baya har ma ya bayar da misalai a cikin wasikar.
Har wayau wasikar ta ce ana ganin laifin shugaban jam'iyyar ta PDP to amma da bazar gwamnati ce yake rawa. Wasikar ta cigaba da cewa idan an ga laifin barawo shi mai bin sawu ba za'a kyaleshi ba. Kana wasikar ta ce kada shugaba Jonathan ya manta fa sun cimma matsaya cewa wa'adi guda ne zai yi akan mulki.
Daga nan ne siyasar Jonathna ta cigaba da samun cikas har ya fadi zabe a 2015.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng