2019 : Hadda 'yan APC a cikin 'yan takara guda bakwai da jam'iyyar PDP take so ta tsayar da su takarar shugaban kasa a zaben 2019 - PDP

2019 : Hadda 'yan APC a cikin 'yan takara guda bakwai da jam'iyyar PDP take so ta tsayar da su takarar shugaban kasa a zaben 2019 - PDP

- Jam'iyyar PDP ta lissafo mutane bakwai da ta ke son tsayar da su takarar shugaban kasa a 2019

- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da wani gwamna na jam'iyyar APC suna daga ciki mutane bakwai da PDP take son ta tsayar da su takara

Yayin da aka fara shirye-shiryen zaben 2019, Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bayyana mutane bakwai da take tunanin za su iya kalubalantar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben shugaban kasa da za a gudanar a 2019.

Jam’iyyar PDP ta bayyana sunayen ‘yan takara da zata tsayar a zabe ko da shugaban kasa Muhammadu Buhar zai kara tsaya takara ba.

Legit.ng ta samu rahoton cewa PDP ta na sa rai akan mutane guda biyar daga cikin jam’iyyar sai kuma mutane biyu daga jam’iyyar APC.

2019 : PDP ta na son ta tsayar da wani gwamna da Sanata daga jam’iyyar APC takarar shugaban kasa
2019 : PDP ta na son ta tsayar da wani gwamna da Sanata daga jam’iyyar APC takarar shugaban kasa

Jam’iyyar PDP tana sa rai jiga-jigan APC guda biyu za su dawo cikin su wanda ya hada da, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da kuma wani gwamna dake kan mulki a yanzu.

KU KARANTA : Gwamna Samuel Ortom yayi gargadi akan satar shanu da daukar fansa

A cikin ‘yan jam’iyyar PDP da ake sa ran za su tsaya takarar shugaban kasa, akwai tsohon mataimakin shugabn kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, Sanata Ahmed Makarfi, tsohon gwamnan jihar Kano, Mallam Ibrahim Shekarau da gwamnan jihar Gombe brahim Dankwambo.

Wani jigo a jam’iyyar PDP ya fadawa manema labaru cewa PDP za ta tsayar da daya daga cikin mutane bakawai da ta lissafo takara ko da Buhari ba zai kara tsayawa takara ba, amma jam’iyyar ta fi son ta tsayar da Atiku.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng