Muna jin dadin goyon baya da gudumawar da mai girma gwamna yake bayarwa ga bangaren tsaro - Kwamishinan yan sandan jihar Bauchi

Muna jin dadin goyon baya da gudumawar da mai girma gwamna yake bayarwa ga bangaren tsaro - Kwamishinan yan sandan jihar Bauchi

Dawowar Mai girma Gwamna Jihar Bauchi Mohammed A. Abubakar Esq keda wuya ya fara karban bakunci daga rundunar ‘yan Sanda ta Jiha.

Yayin karban tawagar, Mai girma Gwamna ya yaba da yadda Jami'an yan Sanda ke aiki don ganin tsaro ya dore a fadin Jiha.

Yace hatta bace-bacen mutane da kaya hade kisan rayuka sunyi sauki a Jihar. Gwamna yayi musu godiya sannan yayi maraba da Mataimakan kwamishanan yan sandan da aka kawo sabbi aiki Jihar Bauchi su uku.

Ya kuma kara da alwashin cigaba da bada kulawa da goyon bayar Gwamnatin sa ga Jami'an tsaro don samun walwalan al'ummar Jihar Bauchi.

Muna jin dadin goyon baya da gudumawar da mai girma gwamna yake bayarwa ga bangaren tsaro - Kwamishinan yan sandan jihar Bauchi
Muna jin dadin goyon baya da gudumawar da mai girma gwamna yake bayarwa ga bangaren tsaro - Kwamishinan yan sandan jihar Bauchi

A jawabin Kwamishinan yan Sanda na Jihar Bauchi, yace sunzo gidan Gwamnatin Jiha wajen Mai girma Gwamna don gabatar masa da wasu manyan Jami'an yan Sanda da Hukumar Ofishin su ta Kasa ta turo su don taimaka masa wajen dorewar zaman lafiya a Jihar Bauchi.

KU KARANTA: APC za ta tsaida mai ba El-Rufai shawara a matsayin Sanatan Kaduna

Kwamishinan yace ya samu karin Mataimaka ne guda uku masu kula da wasu bangarori na tsaro a Hedkwatar Hukumar dake cikin garin Bauchi.

Muna jin dadin goyon baya da gudumawar da mai girma gwamna yake bayarwa ga bangaren tsaro - Kwamishinan yan sandan jihar Bauchi
Muna jin dadin goyon baya da gudumawar da mai girma gwamna yake bayarwa ga bangaren tsaro - Kwamishinan yan sandan jihar Bauchi

Kwamishinan yayi godiya matuka bisa yadda Mai girma Gwamna yake basu hadin kai suke gudanar da aikin su cikin sauki. Sannan sai ya kara da bada tabbacin zage damtse wajen cigaba da samar da tsaron dukiyoyi da rayukan al'ummar Jihar Bauchi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a

https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a

http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng