LABARI DA DUMI-DUMI: Babban darektan yakin neman zaben Dankwambo ya fice daga PDP

LABARI DA DUMI-DUMI: Babban darektan yakin neman zaben Dankwambo ya fice daga PDP

Babban darektan yakin neman zaben gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo na jihar Gombe a zaben 2015, sanata Sa'idu Umar Kumo, ya ce bisa ga alamu gwamnan ba ya bukatarsa a PDP saboda haka ya tara nasa da nasa ya bar jam’iyyar.

Babban darektan yakin neman zaben gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo a zaben 2015, sanata Sa'idu Umar Kumo, ya fice daga jam'iyyar PDP a ranar Litinin, 22 ga watan Janairu.

Kamar yadda Legit.ng ke da labari, sanata Kumo wanda ya wakilci Gombe ta tsakiya a majalisar dattijai tsakanin 1999 zuwa 2003, ya sanar da janye membobinsa daga jam’iyyar PDP yayin da yake ganawa da manema labarai a gidansa da ke Gombe, babban birnin jihar.

Ya ce ya bar jam'iyyar ne saboda rashin jituwa tsakaninsa da gwamna Dankwambo wanda ya yi wa zargin cewa yana kokarin korar sa daga PDP.

Gombe: Babban darektan yakin neman zaben Dankwambo ya fice daga PDP
Gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo

Kumo ya ce zai rubuta wasika ga shugabannin jam’iyyar daga mazabarsa har zuwa jiha don sanar da su a kan shawarar ficewa daga jam'iyyar.

KU KARANTA: Zan cigaba da yin bakin kokari na a kan mulki - Inji Shugaba Buhari

"Ina jin cewa gwamna Dankwambo da wakilinsa ba su a bukata na a PDP, wadanda suka hada kai tare don tilasta ni barin jam'iyyar”.

"Saboda haka, na bari don in ba da dama ga duk waɗanda suke jin cewa ni ke tare musu wuri", inji shi.

Sanata Sa'idu Kumo, ya ce yana tattaunawa ne tare da magoya bayansa a duk fadin kasar a kan makomar siyasarsa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel