Ke Duniya: Al’adar wasu ƙauyawa dake kashe ýan biyu da Zabiya a babban birnin tarayya Abuja

Ke Duniya: Al’adar wasu ƙauyawa dake kashe ýan biyu da Zabiya a babban birnin tarayya Abuja

Ashe har yanzu halayyar nan da aka sha fama da shi a garin Kalaba na kashe yan biyu, na cigaba da samuwa a babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda jaridar The Nation ta bankado.

Wannan mummunan lamari yayi Kamari a wasu kauyukan dake karamar hukumar Bwari na garin Abuja, wasu daga cikin kauykan sun hada da Gbajingala na yan kabilar Bassa Kuomo, Gurara, Kulo, Gawu, Sabo, Guabe da Chibiri.

KU KARANTA: Yan bindiga sun yi garkuwa da jigogin jam’iyyar APC guda 7 a jihar Neja

Majiyar Legit.ng ta ruwairo sauran kauyukan sun hada da Tekpese, Gurugi, Fuka, Lapa da Dogonruwa na karamar hukumar Kwali sai kuma kauykan Kaida da Kutara duk a karamar hukumar Buari.

Ke Duniya: Al’adar wasu ƙauyawa dake kashe ýan biyu da Zabiya a babban birnin tarayya Abuja
Yan biyu

Al’adar mutanen ta haramta haihuwar yan biyu, zabiya, jarirai masu nakasa da kuma duk jaririn da mahaifiyarsa ta rasu a yayin haihuwarsa, don haka duk jaririn da ya fada cikin jerin nan sai sun kashe shi. Amma wasu su kan kashe jariri daya daya ne su bar daya idan tagwaye ne.

Majiyar ta kara da cewa ana kashe jariran ne saboda a cewarsu ire iren jariran nan na dauke da wasu muggan aljanu, wand aka iya cutar da mutanen kauyen, shi yasa ake sanya musu guba a abinci, ko a yanka su, ko kuma danne musu hanci.

Wata mata mai suna Mama Habiba wanda take aure wani dan kabilar Bassa Kuomo, ta bayyana cewa a haka ta yi asarar jariranta guda uku sakamakon wannnan mummunan al’ada, da wannan ne ya sa Mama Habiba ta kashe aurenta da mijin ta yi sallama daga garin.

Ita kuwa wata mata mai suna Amina ta tsere daga kauyen Gurara tare da Mijinta tun bayan data samu juna biyu, kuma aka tabbatar mata jarirai zata haifa a Asibiti, inda suka koma jihar Neja, a yanzu haka jariransu Jamila da Jamilu sun girma.

Da aka tambayeta ko zasu koma kauyen tunda yaran sun girma, sai tace a’a ba zasu koma ba, don ko a haka yan kauyen zasu iya kashe mata yara, “Musamman na fi tsoron su sa musu guba a abinci.” Inji Amina.

Ku biyo mu a c

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng