Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

- Gwamnatin Katsina ta ce ta kammala shirin daukar malaman makarantun firamare 5,000

- Gwamna Masari ya ratsar da sabon kwamishinan ilimi a yau Litinin a Katsina

- Gwamnan ya ce za a fara daukar malaman makarantun a cikin farkon kwata na 2018

Gwamnatin jihar Katsina ta ce za ta dauka malaman makarantu fiye da 5,000 a makarantun firamare na jihar don bunkasa ma'aikatan ilimi.

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya bayyana hakan a bikin ratsar da sabon kwamishinan ilimi, Dokta Badamasi Lawal, ranar Litinin, 22 ga watan Janairu a Katsina.

Masari ya ce za a daukar malaman makarantun a cikin farkon kwata na 2018.

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari

Ya bayyana cewa za a inganta jin dadin malamai don bunkasa halayensu don samar da hidimomin da suka dace.

KU KARANTA: 2019: Zamu cika duk alkawurran da muka yi wa al’ummar Najeriya – In ji Buhari

Gwamna ya ce gwamnatinsa ta ba da kayan aiki a makarantu don inganta koyarwa.

Ya bukaci sabon kwamishinan don magance zaman kashe wando na ma'aikata a ma'aikatar Ilimi ta jihar.

"Ma'aikatar Ilimi ta na da kimanin darektoci 290 masu zaman kashe wando maimakon yin amfani da lokutan wajen koyarwa da kuma ayyukan gudanarwa”, in ji shi.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa nadin Lawal ya biyo bayan dakatar da tsohuwar kwamishinar, Farfesa Halimatu Idris a watan Disamba, 2017.

Har zuwa wannan lokacin Lawal ya kasance babban mashawarci ga gwamna a kan Ilimi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel