Fashola ya ziyarci babban ofishin hukumar EFCC (hotuna)
Rahotanni sun kawo cewa, a ranar Litinin 22 ga watan Janairu, ministan ayyuka, gidaje da wutar lantarki, Babatunde Raji Fashola ya ziyarci babban ofishin hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC).
Ministan ya kai ziyaran ne domin ya duba yadda ayyukan da akeyi ke gudana da kuma abun da ma’aikatarsa za tayi domin inganta aikin da ya rage.
Ya ba da tabbacin cewa tunda gwamnati na kokarin ganin ta yaki cin hanci da rashawa, ya zama dle a tallafawa wannan hukumomin kamar yadda ya bayyana cewa jami’an hukumar na kashe lokacinsu a ofishinsu fiye da iyalansu.
Ga hotunan ziyaran a kasa:
KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa na sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC – Dakingari
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng