Wata cibiyar kimiyya a Najeriya ta hada maganin ciwon Ebola da Malariya
- Cibiyar kimiyya a Najeriya ta hada maganin gargajiyan da zai magance ciwon Ebola da Malairiya
- Ministan kiwon lafiya yayi alkwarin tallawa cibiyar kimiyya a Najeriya kudade dan cigaba da inganta magungunan gargajiya
Cibiyar kimiyya na National Institute for Pharmacutical Research and Development, NIPRD, ta hada magunguna gargajiya guda shida da zai magance cutar Ebola da Malariya a jikin dan Adam.
Cibiyar ta fitar da wannan magunagunan baya ta samu nasara a gwaje-gwajen da ta yi wanda ya tabbatar da inganci magungunan.
Babban hadimin Ministan harkan kiwon lafiya, Kazeem Akintunde, ya bayyana haka a lokacin da ya zanta da manema labaru a ranar Lahadi.
KU KARANTA : Ba wanda zai shiga rigar Buhari a zaben 2019 - Sakon PDP zuwa ga gwamnonin APC
A cikin magungunan da cibiyar ta hada, akwai maganin da zai iya rage karfin kwayar cutar kanjamau a jikin Dan Adam, maganin kyasbi da cizon kwari.
Ministan kiwon lafiya, Isaac Adewole, a lokacin da yake jawabi, yayi wa cibiyar, NIPRD, alkwarin basu tallafin miliyan N100m saboda su cigaba da kafa cibiyar da zata rika gwaje-gwajen magungunan gargajiya a kasar.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng