Ina sane da gwagwarmayar da aka yi tun daga 2003 Inji Shugaban kasa Buhari
- Shugaba Buhari yace yanzu abubuwa sun canza dole yake bi a sannu
- Shugaban kasar ya gana da manyan 'Yan APC irin su Sen Kwankwaso
- A walimar da ya shirya a Aso Villa yace bai manta da mutanen sa ba
Mun ji cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya fadawa manyan 'Yan Jam'iyyar APC cewa bai manta da su ba ko da sun ji yayi shiru bai neme su ba. Shugaban kasar yace yana sane da gwagwarmayar da aka yi a lokacin da su kayi wata walima a fadar Shugaban kasar.
A makon nan ne Shugaba Buhari ya gana da irin su Rabiu Kwankwaso da Orji Uzor Kalu da wasu 'Yan Jam'iyyar sa. Shugaban kasar ya kore zargin cewa yana nuna kabilanci wajen gudanar da sha'anin sa. Shugaba Buhari ya juna cewa Inyamurai sun fi kowa samun tsokar Ministoci a Gwamnatin sa.
KU KARANTA: An kira Sanata Kwankwaso ya hakura da zuwa Kano
Bayan haka ya nuna cewa lokacin da yake yakin neman zabe tun daga 2003 har nasarar sa, manyan Lauyoyin sa a Kotu mafi yawanci Inyamurai ne. Shugaban kasar yace a haka kuma bai samu nasara a Kotun ba duk da Alkalan mutanen Arewa daga Zaria, Jigawa sa Jihar Neja ne kamar sa.
Shugaban kasar ya kuma bayyana abin da ya sa yanzu yake bin komai sannu a hankali. Yace a lokacin Soji ya daure mutane bisa zargin sata har sai sun ceci kan su wanda a karshen shi ma aka daure sa. Shugaba Buhari yace yanzu ya dawo farar hula don haka dole ya ke gudanar da abubuwa a tsanake.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng