Zaben 2019: Kungiyar Dillalan Abinci a Jihar Bauchi za su sayawa Buhari tikitin tsayawa takara

Zaben 2019: Kungiyar Dillalan Abinci a Jihar Bauchi za su sayawa Buhari tikitin tsayawa takara

- Kungiyar Ma su Dafa Abincin Yaran Firamare na Jihar Bauchi ta yi ma Buhari da Gwamnan Jihar mubayi'a

- Kungiyar ta ce a shirye ta ke ta saya ma su takardar tsayawa takara a 2019 don nuna godiyar su ga ayyukan da su ka samu

- Shugaban Kungiyar, Hajiya Kaltume Katagum ta bayyana hakan a karshen wannan mako

Wata Kungiyar Dillalan Abinci a Jihar Bauchi ta yi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Gwamnan Jihar, Mohammed Abdullahi Abubakar su tsaya takaran kujerun su a 2019. Kungiyar ta ce a shirye ta ke ta saya ma su takardun tsayawa takaran.

Shugabar Kungiyar, Hajiya Kaltume Katagum, ita ce ta bayyana hakan a karshen wannan makon yayin ziyarar ban girma da kungiyar ta kai wa mai ba wa Gwamnan shawara ta musamman kan harkokin Kungiyoyi ma su zaman kan su (NGOs), Mansur Manu Soro.

Za mu saya wa Buhari tikitin takarar zabe
Za mu saya wa Buhari tikitin takarar zabe

Katagum ta ce su na son Buhari ya cigaba da kyawawan ayyukan da ya ke yi kamar su samar da tsaro da bayar da tallafi ga al'umma da samar ma su da ayyukan yi. Ta kuma bayyana yadda ciyarwar da a ke yi wa yaran firamare ya samarwa mata ma su yawa ayyukan yi.

KU KARANTA: 'Yan a ware na PDP sunyi sulhu da uwar Jam'iyyar

A cewar ta, mata ma su girka abincin su na samun kudi har naira 100,000 wanda a baya ba su taba samun naira 5,000 na su ba. Hasali ma, ba su taba mu'amala da banki ba sai zaman Buhari Shugaban Kasa.

Don haka ne su ke son su mika godiyar su ta hanyar yi ma sa mubayi'a da tsayawa takara a 2019. Kungiyar ta mika godiyar ta makuka ga duk wadanda su ke da hannun cikin wannan ayyuka da su ka samu. Shi kuma Soro ya yaba da ziyarar da kungiyar ta kai, ya kuma yi ma su albishir da wasu tsare tsaren Gwamnati na tallafi da za su zo nan gaba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: