APC a Katsina ta watsar da yiwuwar zaben kananan hukumomi a jihar

APC a Katsina ta watsar da yiwuwar zaben kananan hukumomi a jihar

- Jam'iyyar APC a Katsina ta yi watsi da yiwuwar gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar

- Jam'iyyar ta ce shugabanin rikon kwarya a kananan hukumomi yafi dacewa don inganta harkokin gwamnati a yankunan karkara

- Shugaban jam'iyyar ya ce wannan mataki ya kasance mai yiwuwa har lokacin da kotu ta yanke hukunci a kan batun

Jam'iyyar APC reshen jihar Katsina ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki a jam’iyyar don tsara hanyoyin da za a yi amfani da su, wajen gudanar da harkokin kananan hukumomi a jihar.

Taron, wanda shugaban majalisar dokokin jihar, Hon. Abubakar Yahaya Kusada, ya jagoranta wanda aka gudanar babban dakin taro na ‘Presidential Banquet’ da ke gidan gwamnati.

Kamar yadda Legit.ng ke da labari, taron ta samu halartar manyan masu ruwa da tsaki a jam’iyyar daga sassan daban-daban na jihar.

APC a Katsina ta watsar da yiwuwar zaben kananan hukumomin don sanya wakilai
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari

A jawabinsa na maraba, shugaban jam'iyyar, shiitu S. Shiitu ya bayyana cewa taron zai yi la'akari da sakamakon kwamitin da gwamnati ta kafa a kan kananan hukumomi wanda shugaban majalisar dokokin jihar ya jagoranci.

KU KARANTA: Yan siyasa na raba kawunan yan Najeriya don son ransu – Gwamnan jihar Ogun

Shiitu ya lura cewa an yanke shawarar a baya cewa nadin shugabanin rikon kwarya a kananan hukumomi yafi dacewa don gudanar da harkokin gwamnati a yankunan karkara.

Shugaban jam'iyyar ya bayyana cewa wannan mataki ya kasance mai yiwuwa har lokacin da kotu ta yanke hukunci a kan shugabancin kananan hukumomin.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng