Kimiyya da Kiwon Lafiya: An gano sabuwar hanyar ganin mafarin cutar daji, wato Kansa

Kimiyya da Kiwon Lafiya: An gano sabuwar hanyar ganin mafarin cutar daji, wato Kansa

- Cutar daji ko Cancer tana da hadari kuma bata da magani

- Musamman idan ba'a gano ta da wuri ba har taci ta cinye

- An ganio sabuwar fasahar ganin alamunta kafin tayi karfi

Kimiyya da Kiwon Lafiya: An gano sabuwar hanyar ganin mafarin cutar daji, wato Kansa
Kimiyya da Kiwon Lafiya: An gano sabuwar hanyar ganin mafarin cutar daji, wato Kansa

Masana kimiyya a kasar Amurka, sun e sun sami gagarumar bulla kan fahimtar alamomin cutar daji watau kansa, mai azabtarwa da kisan miliyoyin mutane a fadin duniya.

Anyi gwaje-gwajen ne kan marasa lafiya dubu daya domn fahimtar irin nau'ukan cutar har guda takwas, kuma an sami gagarumar nasars watau breakthrough a turance.

Gwajin wanda a ka yi wa lakabi da suna CancerSeek ya nuna samun nasara da kashi saba'in cikin dari. Wasu masana sun ce wannan ci gaba na da matukar amfani, sai dai akwai bukatar kara tabbatar da sahihancinsa.

DUBA WANNAN: An harbi mai ciki garin fasa taro

Masu bincike a jami'ar Johns Hopkins sun ce sakamakon abun farin ciki ne kuma zai yi babban tasiri wajen mace-mace a dalilin cutar daji. Burinsu shi ne a rika yin wannan gwaji duk shekara domin a ceto rayukan mutane.

Cutar daji dai bata da magani, amma tarar ta da wuri kan sa a iya qone kwayoyinta, watau halittar mutun ta cells da suka sami tawaya da birkicewa, wadda su suke dunkulewa su zamo kansa, kuma suna bazuwa cikin jiki muddin ba'a tare su ba.

Hanyoyin maganin cutar sun hada da kune wurin da haske, watau laser therapy, sai chemotherapy, wanda shi kuma guba ake maka wa wurin, sai kuma yanke wurin da ya fara rikidewar, kamar nono ko huhu ko yankin kwakwalwa.

Cutar ta fi kama tsofi, amma a zamanin nan har yara tana kama wa, musamman masu cin abu da ba tsirrai na duniya ba, kamar abinci da aka hada da kwayoyin habaka shi, kamar takin zamani, ko chemical don adana abinci ya dade.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: