Hukumar EFCC ta na binciken yadda $500m da Abacha ya sace su ka yi layar zana
- Hukumar ta EFCC ta bayyana yadda a ka ingiza dala miliyan 250 cikin asusun ofishin Dasuki a 2015
- Ofishin Ministan Kudi a karkashin shugabancin Okonjo-Iweala ne ta fitar da wannan kudi
- Don haka ne EFCC za ta gayyato ta don neman bahasi
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), ta fara bincike game da yadda a ka karkatar da dala miliyan 500 da a ka maido su asusun gwamnati a 2015, lokacin shugabancin Jonathan, daga hannun iyalan Sani Abacha.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewar, EFCC ta bayyana yadda a ka ingiza miliyan 250 cikin asusun bankin ofishin Sambo Dasuki yayin da ya ke Mai Bayar da Shawara kan Harkar Tsaro. An turo wannan adadin ne ba tare da bin ka'ida da doka ta tanadar ba, wattani biyu gabanin saukar Jonathan daga mulki.
KU KARANTA: Daliban Jami'ar Jihar Osun sun yanke jiki sun fadi a cikin aji
Sauran miliyan 250 kuwa ba a san inda su ka shiga ba. Ofishin Ministan Kudi a zamanin Okonjo-Iweala ne ta gudanar da wannan fitar kudi bisa umurnin Tsohon Shugaban Kasa Jonathan. An tura wannan kudi ne a wani asusun banki da ke Landan.
Wata majiya daga Hukumar EFCC da ta nemi a sakaya ta, ta bayyana cewar Hukumar za ta gayyato Iweala don bin bahasin kudin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng