Kwana daya bayan taron sulhu a Ekiti, Makiyaya sun kashe wata mata mai ciki

Kwana daya bayan taron sulhu a Ekiti, Makiyaya sun kashe wata mata mai ciki

- Makiyaya sun kai hari wani gari a jihar Ekiti inda suka kashe wata mace mai cikin wata takwas

- Mazaune garin sunyi ikirarin cewa harin ramuwar gayya ne kan kisan wani bafulatani da ake zargin Tibi ne suka kashe shi a Oke-Ako

- Wannan harin dai ya faru ne bayan kwana daya kacal da Gwamna Fayose na Ekiti ya gudanar da taron zaman lafiya tsakanin Fulani da Tibi

Mun samu rahoton rasuwar wata mata mai ciki a ta aka harbe ta bindiga a jihar Ekiti. Matar wadda akace yar asalin kabilan Tibi ne ta gamu da ajalin nata ne a unguwar Orin da ke karamar hukumar Ido/Osi na jihar ta Ekiti.

Wasu mazauna unguwar sunyi ikirarin cewa kisar nata ramuwar gayya ne kan kisa wani bafilatani da ake zargin yan kabilan Tibi ne suka kashe shi a Oke-Ako.

Kwana daya bayan taron sulhu a Ekiti, Makiyaya sun kashe wata mata mai ciki

Kwana daya bayan taron sulhu a Ekiti, Makiyaya sun kashe wata mata mai ciki

KU KARANTA: Filayen jihar Kogi ba mallakar ka bane: Wani Shugaban al'umma ya gargadi Gwamna Bello

Sunce Fulanin sun kai hari kauyen ne cikin dare inda suka harbe matar mai ciki na watanni takwas.

Kisan dai ya faru ne kwana daya bayan taron zaman lafiya da sulhu da Gwamnan jihar na Ekiti, Ayodele Fayose ya kira inda kuma ya gargade wakilan Fulani da Tibi kan kisan ramuwar gayya wadda ka iya tada fitina a Jihar.

Fayose ya shawarci al'umman jihar da su zauna lafiya, bugu da kari, mahalarta taron sun amince da cewa za'a gayyato sauran masu ruwa da tsaki a jihar domin cin matsayar zaman lafiya mai dorewa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel