Gwamnatin Kaduna ta ware naira miliyan 200 domin tallafa wa mata a jihar
Gwamnatin jihar Katuna ta ware kudi kimanin naira miliyan 200 domin bayar da tallafi ga mata a jihar.
Kwamishinan harkokin mata na jihar Kaduna Hafsat Baba, ce ta sanar da wannan ci gaban.
A cewar Hafsat bayan wannan shiri da gwamnati ta yi ma’aikatarta ta gina wuraren koyon sana’a ga mata a jihar har guda uku saboda horar dasu sana’ar hannu.
Sannan kuma ta kara cewa da zaran ma’aikatarta ta kammala shirya ka’ido’jin da duk mai bukatar bashin zai cika kafin ya samu, za ta sanar wa mutane domin su fara karba.
KU KARANTA KUMA: Tattalin arziki: Hannun jarin Najeriya yana cikin mafi Kasuwa a Duniya
Daga karshe ta ce wannan wuraren koyon sana’a zai taimaka wa ba mata ba kawai har da matasa dake sun inganta rayuwar su.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng