Tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido ya caccaki Shugaba Buhari

Tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido ya caccaki Shugaba Buhari

- Sule Lamido yayi kaca-kaca da GwamnatinShugaba Buhari

- Tsohon Gwamnan yace 2019 za a dauki mataki a zaben 2019

- Yace da zarar mutum ya koma APC ya tserewa binciken EFCC

Mun ji cewa tsohon Gwamnan Jigawa Alhaji Sule Lamido ya caccaki Gwamnatin APC ta Shugaba Muhammadu Buhari inda yace har yanzu babu abin kirkin da Jam’iyyar tayi a mulki sai dai kiran abin da za ayi.

Tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido ya caccaki Shugaba Buhari
Lamido yace rashin man fetur ya hana Tinubu zuwa taro

Sule Lamido ya soki Gwamnatin Buhari a wajen wani taro da Daily Trust ta shirya. Manyan ‘Yan siyasar Kasar su ka halarta. Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustafa ne ya wakilci Shugaban Kasa Buhari a taron.

KU KARANTA: Osinbajo da Gwamnoni sun shiga taro a Villa

Alhaji Lamido yace saboda Shugaba Buhari ne Ministan fetur shiyasa Bola Tinubu bai samu zuwa taron ba don kuwa motar sa na layin man fetur a Legas. Lamido yace ya ragewa ‘Yan Najeriya su sake tunani a 2019.

Tsohon Gwamnan yace a lokacin da Marigayi ‘Yaradua yana mulki, Shugaba Buhari bai taba zuwa taron tsofaffin Shugaban kasa ba sai bayan ya rasu sannan ya fara halarta. A jawabin sa ya yabawa Bola Tinubu.

Sule Lamido yace APC ta dauki ‘Yan PDP mutanen banza amma kuma yanzu duk tsofaffin ‘Yan PDP ne su ka cika Jam’iyyar mai mulki. Lamido yace da zarar mutum ya shiga APC, EFCC ba ta binciken sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: