LABARI DA DUMI-DUMI: 'Yan bindiga sun sace ‘yar shekara 14 a Katsina
- Wasu 'yan bindigan sun yi garkuwa da wata ‘yar shekara 14 a Katsina
- Mahaifin yarinyan ya ce 'yan bindiga sun kai hari a gidansa a misali karfe 1:30 na safiyar ranar Alhamis
- Alhaji Salisu ya ce duk abin da ‘yan bindigar suka tambaye shi bai ki amince da bukatunsu
Wasu 'yan bindigan da ba a sani ba sun sace wata yarinya mai shekaru 14 a yankin karamar hukumar Kankia da ke jihar Katsina.
Mahaifin yarinyan da aka sace, Alhaji Salisu Mai-Tiles, ya bayyana cewa 'yan bindigar sun kai hari a gidansa da ke Sabuwar-Abuja a garin Kankia a daidai karfe 1:30 na safe a ranar Alhamis, 18 ga watan Janairu.
Ya ce mutane uku da manyan makamai sun shiga gidansa suka bukaci kudi, yayin da sauran mambobi suka tsaya a waje.
"Sun tambaye ni in ba su kudi, wadda kuma na yi, duk abin da suka tambaye mu ba mu ki amince da bukatunsu ba don ceton rayukanmu , amma duk da hakan sun tafi da 'yata mai shekara 14", in ji shi.
KU KARANTA: Dubi hotunan 'yan ta'adda da suka addabi matafiya a kan hanyar Suleja zuwa Bidda
Majiyar Legit.ng ta tattaro cewa mambobin kungiyar sun katange hanya ta Katsina zuwa Kano a Kankia kuma suka yi wa masu motoci fashi a garin.
A wani bangare kuma ana zargin 'yan fashi da makami sun harbe wani dan sanda har lahira a kusa da WAPA Shopping Mall a Katsina a daren ranar Alhamis kuma suka yi awon gaba da kudaden da ba a adadinsu ba.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng