Bincike ya nuna sanadarin wanke baki zai iya maganin ciwon Malaria
- Masana kimiyya sun gano sabuwar sanadarin dake maganin ciwon malaria
- Kungiyar WHO ta ce akalla mutane ke mutuwa daga cutar malaria a nahiyar Afrika
Binciken da aka gudanar da inji mai aikin da kansa (Robot) an gano cewa sanadarin dake cikin abun wanke baki zai iya maganin ciwon malaria.
Jami’an Cambridge dake kasar Birtaniya ta gudanar da bincike da inji mai aikin da kansa (Robot) wajen gano wani sanadari mai suna, triclosan, dake cikin abun wanke baki zai iya hana malaria shiga jikin dan Adam.
Kungiyar kiwon lafiya na duniya (WHO) ta ce akalla mutane 500,000 ke mutuwa daga ciwon malaria a kowani shekara a nahiyan Afrika wanda mafi akasarin su kanana yara ne.
KU KARANTA : Paul Unongo ya sauka daga matsayin shugaban kungiyar Dattawan Arewa (NEF)
Ana iya maganin ciwon malaria da magunguna da yawa, amma duk duka haka yana fin karfin magugunan, wannan yasa samun maganin ciwon malaria ya fara wuya.
Masana kimiyya sun ce, sanadarin Triclosan dake cikin abun wanke baki yana samar da kwayoyin da za su hana cutar malaria shiga jikin dan Adam.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng