An cafke wani kocin kwallon kafa bisa laifin luwadi da yaro dan shekara 13
Rahotanni sun kawo cewa an kama wani kocin kwallon kafa mai shekaru 19 kan laifin aikata luwadi da wani yaro mai shekaru 13 a jihar Lagas.
Yaron wanda ya bukaci a sirrinta sunansa ya bayyana cewa, kocin ya sha aikata lalata da shi lokuta da yawa, bayan ya gama sai ya bashi ladar naira 100 zuwa 200.
Kocin wanda jagora ne na kungiyar kwallon kafa na matan ‘yan sanda (POWA) ya amsa laifin da cewa, ya yi matukar nadamar aikata wannan mumunar aiki, kuma ba komai ya kai shi ga haka ba illa sharrin shedan.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: A yau Buhari zai karbi sabbin Jakadai daga kasashen waje guda
Da ake tuhumar mahaifiyar wannan kocin, ta ce tun ba yau ba danta ya ke fama da wannan jarabawar, ta kai shi coci bayan da aka kama shi da irin wannan laifin a shekarar 2016.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng