Labarun Kannywood: Da aurena nake yin fina finan Hausa – Inji Daso

Labarun Kannywood: Da aurena nake yin fina finan Hausa – Inji Daso

Shahararriyar jarumar fina finan Kannywood, Saratu Gidado wanda aka fi sani da suna Daso ta tabbatar da cewa ta dade tana Fim duk dayake tana da aure, ta bayyana cewar shi Fim ai fadakarwa ne.

Daso ta bayyana haka ne cikin hira da tayi da gidan rediyon BBC Hausa, inda tace jama’a da dama suna nuna mata tsangwama, a sanadiyyar irin rawar da take takawa a Fina finai, wanda baya ma masu kallo dadi.

KU KARANTA: Daliban jihar Kaduna sun yi madalla da matakin sallamar Malamai a jihar

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Daso tana fadin sau dayawa mutane su kan yi mata mummunan zato, tare da nuna bacin ransu game da wani mummunan hali da ta nuna a cikin Fim, sai dai tace a duk lokacin da ta gamu da irin hakan, sai dai ta basu hakuri, tare da shaida musu a wasa ne, ba gaskiya bane.

Labarun Kannywood: Da aurena nake yin fina finan Hausa – Inji Daso
Saratu Daso

Da aka tambayeta game da aure, sai tace: “Na dade da aurena nake yin Fim, mijina ya amince min, don haka ina yin Fim kama yadda mata zata fita gidanta ta tafi wajen aiki.” Sa’annan ta kara “Mijina wayayye ne, dan Boko ne, kuma Malamin addini ne, don haka idan ya ganni a Fim baya jin komai, ya san ba da gaske bane.”

Sai dai Hajiya Saratu tace a yanzu ba zata dinga fitowa a irin wasu halaye ba, kamar mutum ya dinga ihu, ko zurawa a guje, da dai makamantansu, don a yanzu gira yazo, don haka sai dai ta dinga taka rawar nutsuwa, a cewarta.

A baya dai, kafin shigar harkar Fim, Daso ta kasance Malamar makaranta ce, amma bayan shigarta Kannywood, sa tauraruwarta ta haskaka sosai, har ma ta yi wasu fina finan turanci.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng