Kungiyar Miyetti Allah ta gabatar da muhimmin bukata a gaban shugaba Buhari

Kungiyar Miyetti Allah ta gabatar da muhimmin bukata a gaban shugaba Buhari

Kungiyar Miyetti Allah ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya hukunta wadanda suka hallaka makiyaya.

A wata sanarwa dauke da sa hannun babban sakataren kungiyar na kasa, Alhaji Baba Usman Ngeljarma a ranar Laraba, 17 ga watan Janairu ya ce, kiran martani ne ga tabbacin da shugaban kasa Buhari ya bayar na kama tare da hukunta wadanda suka aiwatar da kisan Benue.

Kungiyar ta Miyetti Allah ta roki shugaban kasar da ya yi amfani da matsayinsa na adalin shugaba wajen kama wadanda suka aikata kisan kiyashi a Mambila, Numan da kuma Kajuru.

Kungiyar ta yi kira ga shugaban kasar da ya tabbatar da adalci da daidaito wajen hukunta masu laifin ba wai na kisan Benue ba harma da na Mambila.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan sanda sun kama mutane uku kan tashin bam din Edo

Daga karshe kungiyar ta yi Allah wadai da kisan kiyashin da akayi a jihar Benue sannan kuma ta ba shugaban kasar tabbacin samun goyon bayanta da hadin kai a kokarinsa na dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin Najeriya

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng