Zargin badakalar N450m: Baban Lauya ya ce babu tuhuma a kansa, ya bukaci kotu ta sallame shi

Zargin badakalar N450m: Baban Lauya ya ce babu tuhuma a kansa, ya bukaci kotu ta sallame shi

- Ana tuhumar lauya Dele Belgore da badakalar kudi, miliyan N450

- Ya bukaci kotu ta yi watsi da karar

- Hukumar EFCC ce ta gurfanar da lauyan gaban kotu

Babban lauyan Najeriya mai lambar girma ta SAN, Dele Belgore, ya fadawa kotu cewar babu tuhuma a kansa, a saboda haka kotu ta sallame shi kawai ya yi tafiyar sa. Belgore na neman kotun ta yi watsi da laifin almundahanar kudi, miliyan N450, da hukumar yaki da cin hanci (EFCC) ke tuhumar sa da hannu a ciki.

Kazalika, mutumin da hukumar EFCC ke zargi da hada baki da babban lauyan wajen aikata almundahanar kudaden, Farfesa Abubakar Sulaiman, tsohon ministan tsare-tsare na kasa, ya mikawa kotu takarar neman ta yi watsi da tuhumar da ake yi masa.

Hukumar EFCC na zargin lauya Belgore da tsohon minista Sulaiman da karbar kudi Naira miliyan 450 daga hannun tsohuwar ministar man fetur, Diezani, gabanin zaben shekarar 2015.

KU KARANTA: Hukumar NSCDC ta gano dabarun masu sayar wa Boko Haram man fetur

EFCC tana tuhumar su da karbar kudin ba tare da kudin sun bi ta wata kafar hada-hadar kudade ba, yin hakan ya sabawa dokokin da suka haramta safarar kudi, a cewar EFCC.

Lauyan hukumar EFCC ya shaidawa kotu cewar, Belgore da Sulaiman sun aikata laifukan da suka saba da sashe na 1(a), 16(d), 15(2)(d) da 18(a) na sabon kundin haramta safarar kudi na shekarar 2012.

An fara gurfanar da wadanda ake tuhumar be a gaban wata babbar kotun gwamnatin tarayya dake Legas a ranar 8 ga watan Fabrairun shekarar 2017.

Saidai wadanda ake tuhumar sun musanta zargin da hukumar ke yi masu.

Bayan gabatar da shaidu da kuma hujjoji, hukumar EFCC ta bayyanawa kotu cewar ta kammala gabatar da kara, tare da bayar da dama ga wadanda ake tuhuma su kare kansu.

Saidai bayan dawowar zaman kotun a yau, Talata, 16 ga Janairu, 2018, masu kare wadanda ake tuhuma, Ebun Shofunde da Olatunji Ayanlaja, sun fadawa kotu cewar babu tuhuma a kan wadanda suke karewa, sannan suka bukaci kotu da ta yi watsi da karar.

Alkalin kotun, Rilwan Aikawa, ya daga sauraron karar ya zuwa 15 ga watan Fabrairu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel