Illolin shan kwayar maganin Paracetamol ba kan ka'ida ba - Masana
- Shugaban Kungiyar masana kimiyan magunguna ya fadakar da al'umma kan iloloin ta ke tattare da amfani da kwayar Paracetamol ba bisa ka'ida ba
- Mista Jelili Kilani ya ce amfani da kwayar ta Paracetamol ba bisa ka'ida ba na yin lahani ga hanta da kodar dan adam
- Kilani ya ce galibi lahanin na bayyana ne bayan an dauki lokaci mai tsawo a jikin dan adam, kuma ya shawarci al'umma su rika tuntubar likoci
Kungiyar masana kimiyan magunguna na Najeriya ta yi gargadi kan amfani da kwayoyin maganin ciwon kai da zazabi wato Paracetamol ba kan ka'ida ba domin hakan na yin lahani ga hanta da kodar dan-adam.
Ciyaman din kungiyar, reshen Abuja, Mista Jelili Kilani ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da kamfanin dillanci labarai (NAN) a ranar Talata a babban birnin Tarayya Abuja.
DUBA WANNAN: Gwamnatin Tarayya ta kashe N35bn wajen biyan kudaden ariya ga na ma'aikata
Mista Kilani shan magunguna fiye da yadda ka'idar ta yake ko kuma yin amfani da maganin ta hanyoyin da bai dace ba na da matukar hadari kuma galibi mutum ba zai ga illar nan ta ke ba sai bayan wasu yan shekaru.
Mr Kilani ya yi kira da al'umma su guji shan kwayoyin maganin na Paracetamol ba bisa ka'ida ba domin kaucewa yin lahani ga jikin su. Ya ce maganin da bai da illa ga jikin dan adam shine ruwa.
Daga karshe Kilani ya shawarci al'umma su tutunbi likita idan sun sha magananin na Paracetamol sau daya amma zazabin bai tsaya ba a maimakon cigaba da shan maganin na lokaci mai tsawo.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng