Kwamishinan Ganduje ya amsa tambayoyi a hannun yan sanda kan wani bidiyo da ya saki game da Kwankwaso

Kwamishinan Ganduje ya amsa tambayoyi a hannun yan sanda kan wani bidiyo da ya saki game da Kwankwaso

- Rundunar yan sandan jihar Kano sun maida martini akan wani bidiyon batanci ga tsohon gwamna Rabiu Kwankwaso da ya shahara

- Jami’in ya gayyaci kwamishinan ayyuka na musamman na jihar Abdullahi Abbas kan bidiyon kiyayya ga Kwankwaso

- An gayyaci Abbas ne bayan wani takardan korafi da wani lauya mai zaman kansa ya gabatar

Rundunar yan sanda reshen jihar Kano, a jiya, ta binciki Kwamishinan harkoki na musamman na Gwamna Abdullahi Ganduje, Alhaji Abdullahi Abbas, akan wani bidiyo mai manufar zuga mutane akan sanata Rabiu Kwankwaso.

Haduwar Abbas da yan sandan ya biyo bayan kame yaransa biyu da wata ma’aikaciyar gidan bisa al’amarin rashin jituwa tsakanin magoya bayan Ganduje da Kwankwso da ya auku a ranar Lahadi.

Kwamishinan Ganduje ya amsa tambayoyi a hannun yan sanda kan wani bidiyo day a saki game da Kwankwaso
Kwamishinan Ganduje ya amsa tambayoyi a hannun yan sanda kan wani bidiyo da ya saki game da Kwankwaso

Yayinda yake gabatar da jawabai ga manema labarai akan tashin hankalin siyasa a jihar, da kuma hanyoyin magance al’amarin mai magan da yawun yan sanda a Kano, DSP Magaji Majia, yace gayyatan kwamishinan ya biyo bayan wata rubutacciyar kara da wani lauya mai zaman kanshi ya gabatar.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar MURIC ta caccaki gwamnatin tarayya kan bayar da kyautar N40m ga tsofaffin shugabannin kasa

Ya bayyana cewa asalin yaransa biyu da aka kama a matsayin Sani Abbas da Abbas Abbas, sannan ma’aikaciyar a matsayin Nazeephy Shawuya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng