Yanzu-yanzu: Boko Haram ta kai sabon hari jihar Adamawa

Yanzu-yanzu: Boko Haram ta kai sabon hari jihar Adamawa

- Yan tada kayar bayan Boko Haram sunyi garkuwa da mutane jiya

- Wannan ya faru ne bayan sun saki bidiyon da ke nuna yan matan Chibok

Mutane da dama sun hallaka, an yi garkuwa da wasu a sabuwar harin da yan kungiyar Boko Haram suka kai ungiwar Pallam da ke karamar hukumar Madagali a jihar Adamawa.

Rahoto ya nuna cewa sai aka kwashe sa'o'i biyar yan ta'addan na aika-aika.

Wannan hari ya zo ya faru kimanin mako daya kenan bayan yan ta'addan sun kai irinsa a unguwannin Wanu, Kamale, da kafin Hausa a Michika da Madagali.

Pallam garin mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Adamawa, Emmanuel Tsamdu. ne.

Yanzu-yanzu: Boko Haram ta kai sabon hari jihar Adamawa
Yanzu-yanzu: Boko Haram ta kai sabon hari jihar Adamawa

Wani mazaunin garin, Abamu Japhet yace: " Sun silalo garin Pallam misalin karfe 11 na dare kawai suka fara harbin kan mai uwa da wabi tare da kona gidaje."

"Da kyar na samu na gudu wajen buya kafin na tsira; babu wani sojan da ya kawo mana agaji. A yanzu dai bamu san yawan mutanen da aka kashe ba amma abun ba dadi."

KU KARANTA: Hotunan bukin zagayowar ranar haihuwa na diyar Ali Nuhu, Fatima

Tabbatar da wannan harin, wani da majalisan wakilan da ke wakilta Madagali da Michika, Adamu Kamale, yace yan ta'addan suna hallaka dabbobi, sun yi fashi, da kona gidaje

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a

Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma

Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labaran Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng