Yan sanda sun kama A'isha Buhari ta karya a garin Abuja

Yan sanda sun kama A'isha Buhari ta karya a garin Abuja

Jami'an 'yan sandan Najeriya shiyyar garin Abuja, babban birnin tarayya sun bayyana samun nasarar cafke wata mata mai suna Aisha Bello mai shekaru 37 a duniya bisa ga laifin badda-kama da sunan uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari.

Yayin da yake bayyana matar ga manema labarai jiya a Abuja, kwamishinan 'yan sandan garin na Abuja, Sadiq Bello ya bayyana cewa ita matar ta kware ne wajen yin anfani da sunan Aisha Buhari din don ta damfari al'umma.

Yan sanda sun kama A'isha Buhari ta karya a garin Abuja

Yan sanda sun kama A'isha Buhari ta karya a garin Abuja

Legit.ng ta samu haka zalika cewa 'yan sandan sun ce sun gano layin wayar salula a hannun matar da tayi rijista da shi da sunan Aisha Buhari din.

Haka zalika binciken farko-farko na jami'an 'yan sandan ya tabbatar masu da cewa matar ta fito ne daga jihar Filato dake a yankin Arewa ta tsakiya sannan kuma tana da 'ya'ya hudu.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel