Kungiyar HURIWA ta gargadi Kwankwaso akan ziyarar jihar Kano

Kungiyar HURIWA ta gargadi Kwankwaso akan ziyarar jihar Kano

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta HURIWA (Human Rights Writers Association of Nigeria), ta gargadi sanata Rabi'u Musa akan ya dakatar da aniyyarsa ta kai ziyara jihar Kano a ranar 30 ga watan Janairu wadda kungiyar Kwankwasiyya ta shirya.

Shugaban wannan kungiya na kasa, Emmanuel Onwubiko, shine ya bayyana hakan a wata sanarwar ranar Litinin din da ta gabata, inda yake jin tsoron salwantar rayuka a sanadiyar arangama tsakanin magoya bayan gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje, wato 'yan Gandujiyya da kuma 'yan Kwankwasiyya a yayin ziyarar.

Sanata Rabi'u Kwankwaso
Sanata Rabi'u Kwankwaso

Wannan sanarwar tazo ne a sakamakon arangamar da ta afku a tsakanin magoya bayan Kwakwaso da na Ganduje a karshen makon da ya shude.

KARANTA KUMA: Ka manta da 2019, magance rikicin makiyaya shine muhimmi a gabanka - Shehu Sani ga Buhari

Kungiyar kare hakkin take cewa, wannan lamari barazana ce mai matukar girma na bayar da izinin aiwatar da kowane nau'i na siyasa da zai gadar da rikici a tsakankanin al'umma.

Kungiyar ta kara da cewa, ya kamata Kwankwaso yayi karutun ta nutsu tare da hangen nesa wajen dakatar da wannan ziyara domin kaucewa barna, tare da cewar hukumar zabe ta kayyade watan Agusta a matsayin lokacin da a iya fara gudanar da yakin zabe a kasar nan.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel