Har gobe, ba mu yi wa Rahma Sadau afuwa ba – MOPPAN

Har gobe, ba mu yi wa Rahma Sadau afuwa ba – MOPPAN

- Kungiyar MOPPAN tace har yanzu ba a yafewa Rahma Sadau ba

- Kabiru Maikaba yace ba Afakallahu bane zai yi wa ‘Yar afuwa ba

- Kwanan nan za a zauna da babbar ‘Yar wasan kwaikwayon a Kano

Mun samu labari a makon nan cewa Kungiyar MOPPAB ya ‘Yan wasan Najeriya tace har yanzu fa ba ta yafewa ‘Yar wasan nan ta Hausa da ta dakatar a da can ba watau Rahma Sadau ba.

Har gobe, ba mu yi wa Rahma Sadau afuwa ba – MOPPAN

Kai ya rabu game da yafewa Rahma Sadau

Kungiyar MOPPAN ta Jihar Kano ta musanya cewa ta gafarta Rahma Sadau laifin ta kuma an yafe mata ta rika fitowa a fina-finan Kannywood. Shugaban MOPPAN na Jihar Alhaji Kabiru Maikaba yace ba a yafewa ‘Yar wasar ba tukun.

KU KARANTA: EFCC ta kara maka Matar Jonathan a Kotun Legas

A baya dai Shugaban Kungiyar tantance fina-finan Hausa Isma’ila Na’abba Afakalla yace Kungiyar su ta shirya tantance fina-finan ‘Yar wasar da aka dakatar kwanaki wanda hakan ya sa aka dauka an yi wa Sadau din afuwa ne.

Maikaba ya bayyana sashen Hausa na BBC a yau dinnan cewa kwanan nan za su zauna da ‘Yar wasan bayan ta dawo kasar wajen da ta tafi. Bayan zaman ne za a san matakin da za a dauka game da Tauraruwar ‘Yar wasar Hausan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel