Mutane 5 sun mutu a wani karo da kungiyoyin musulunci biyu suka yi a jihar Niger
Akalla mutane biyar ne suka mutu sannan da dama sun ji rauni a wani rikici da ya barke tsakanin kungiyoyin Musulunci gida biyu a karamar hukumar Munya dake jihar Niger a makon da ya gabata.
An ba wadanda suka ji rauni kulawa sakamakon harbin bindiga a wani asibitin kudi dake Sarkin Pawa hedkwatar karamar hukumar da kuma abitin gwamnati dake Gwada yan kilomita kadan daga garin Guni inda rikicin ya barke.
Jaridar Thisday ta rahoto cewa yan sanda sun kama mutane da dama a sarkin-pawa sannan kuma aka kai su hukumar binciken masu laifi a hedkwatan yan sandan.
Rikicin ya afku ne tsakanin yan Darikah da Izala kan lokacin sallatar Juma’a da kuma shawarar da yan Izala suka yanke na samun wajen sallah daban a garin.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari, Gwamna Ortom da dattawan Benue na cikin ganawa mai muhimmanci (bidiyo)
Anyi amfani da muggan makamai ciki harda bindigogi wanda ya haddasa gaggarumin tashin hankali.
An tattaro cewa kungiyoyin biyu sun samu sabani ne lokacin da bangare guda suka ce basu yarda a yi sallar jam’I da karfe 12:30 na ran aba sannan suka yi kokarin hana dayan bangaren yin sallah a wannan lokaci.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng