Buhari ya rikitawa masu neman takarar shugaban kasa lissafi
- Ana tunani Shugaban Kasa Buhari zai sake neman takara a zabe mai zuwa
- Ba haka wasu Gwamnoni da manya a Jam’yyar su ka so ba a halin yanzu
- Akwai wasu ‘Yan Jam’iyyar a Arewa da ke sa ran kujerar Shugaban kasar
Mun fara samun labari cewa lissafin wasu manyan ‘Yan Jam’iyyar APC ya fara birkicewa yayin da aka dumfari zaben 2019 gadan-gadan. A da wasu na tunani Shugaba Buhari ba zai sake takara ba.
Kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar Tribune, Jam’iyyar APC na shirin tsaida Shugaba Buhari ne a matsayin ‘Dan takarar ta na zabe mai zuwa. Hakan dai ya rikita lissafin wasu da ke harin kujerar Shugaban kasar a zabe mai zuwa.
KU KARANTA: Shugaba Buhari ya gana da Gwamnan Jihar Benuwe
Idan har Shugaban kasar ba zai sake neman takara ba dai ana tunani za a nemi ta tsaida Bola Tinubu ne a matsayin ‘Dan takarar ta. Sai dai da dama a Jam’iyyar irin su wani Gwamna da wasu tsofaffin Shugabannin Majalisa ba su so haka ba,
Majiyar tace babu abin da ya fi wa Jam’iyyar irin ta marawa Shugaba Buhari baya a 2019. Babban Jigon Jam’iyyar Bola Tinubu na sa rai cewa Shugaban kasar zai sauka a 2023 ya ba Yarbawa kujerar domin su taka irin rawar su.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
S
Asali: Legit.ng