Fastocin takarar Shehu Sani a jam'iyyar PRP sun bayyana a bainar jama'a

Fastocin takarar Shehu Sani a jam'iyyar PRP sun bayyana a bainar jama'a

Jama'ar Najeriya dai musamman ma na arewaci sannan kuma mazauna garin Kaduna sun cika da al'ajabi bayan da wasu hotunan takarar siyasa na fitaccen dan gwagwarmayar nan Sanata Shehu Sani suka bayyana a bainar jama'a.

Mun samu dai cewa fastocin da suka bayyana din na jam'iyyar PRP ce mai makulli ba jam'iyyar sa ta yanzu ba kamar dai yadda muka samu labari.

Fastocin takarar Shehu Sani a jam'iyyar PRP sun bayyana a bainar jama'a
Fastocin takarar Shehu Sani a jam'iyyar PRP sun bayyana a bainar jama'a

Legit.ng dai haka zalika ta samu cewa a jikin fastocin babu rubutun mukamin da Sanatan ke nema wanda hakan ne ma ya kara jefa mutane cikin rudani da al'ajabi gami da kokwanto.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa Sanata Shehu Sani dai dan majalisa ne yanzu haka dake wakiltar mazabar jihar Kaduda ta tsakiya sannan kuma yana matukar adawa da gwamnan jihar Malam Nasir El-Rufai musamman ma game da korar ma'aikan da yayi a 'yan kwanakin nan.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng