Soyayyar Buhari: ‘Ban taɓa sha’awar auren Buhari ba’ – Inji Fati Shu’uma

Soyayyar Buhari: ‘Ban taɓa sha’awar auren Buhari ba’ – Inji Fati Shu’uma

Shahararriyar jarumar nan ta fina finan Kannywood, Fati Shu’uma ta musanta labarin da ake yadawa na cewa wai tana da sha’awar auren shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Legit.ng ta samu faifain bidiiyo inda jarumar ta musanta labarin, kuma ta tabbatar da cewar bata taba yin hira da wata jarida ko kafar watsa labaru a kan wannan batu ba.

KU KARANTA: Labari da Duminsa: Anyi jina-jina a sabon rikici tsakanin 'yan Gandujiyya da 'yan Kwankwasiyya a jihar Kano

“Assalamu alaikum, sunana Fati, wanda aka fi sani da Fati Shu’uma, naga wani Posting da wata jaridar Mikiya ta yi a shafin Facebook, inda take cewa wai tayi hira da ni,kuma nace babban burina shine in auri shugaban kasa Baba Buhari, karya ne, karya ne, kuma karya ne.” Inji Fati.

Soyayyar Buhari: ‘Ban taɓa sha’awar auren Buhari ba’ – Inji Fati Shu’uma
Fati Shu’uma

Fati ta tabbatar da soyayyar da take yi ma Buhari kamar kowane dan Najeriya dake sonsa, wanda hakan ne ma ya sanya ta zabe shi, amma bata da wani burin aurensa, soyayyar bata kai haka ba.

Daga karshe shu’uma ta bukaci masoyanta da su taimaka mata wajen musanta wannan labarin kanzon kurege, wanda tace bas hi da reshe balle makama.

Ga bidiyon nan:

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng