An kashe mutane 10 a wani harin da aka kai a Kaduna

An kashe mutane 10 a wani harin da aka kai a Kaduna

- Kimanin mutane 10 ne suka halaka a wani harin da aka kai a kauyukan Kaduna

- Hare-haren sun faru a daren ranar Juma'a da ta gabata a kauyukan Dangaji da Ungwan Gajere

- Kakakin hukumar 'yan sandan jihar Kaduna, ya tabbatar da harin, amma ya ce mutane biyar kawai aka kashe

Kimanin mutane 10 ne suka halaka a lokacin da wasu 'yan bindiga da ba sani ba suka kai hari kan kauyuka guda biyu a yankin karamar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.

Rahotanni sun nuna cewa hare-haren sun faru a daren ranar Juma'a, 12 ga watan Janairu a kauyukan Dangaji da Ungwan Gajere.

Kamar yadda Legit.ng ke da labari , bayan wadanda suka mutu a harin, wasu mutane da dama sun samu raunuka daga harbin bindiga yayin harin.

An kashe mutane 10 a wani harin da aka kai a Kaduna

Wasu 'yan bindiga

Al’ummar kauyukan sun tsere don kare rayukansu yayin da ‘yan bindiga suka kone gidajensu.

KU KARANTA: Kashe-Kashe: Kwamitin majalisar dattawa ya dirfafa a jihar Benue

"Abin takaici ne tun daga daren ranar Juma'a mun fuskanci harin wasu ‘yan bindiga da ba’a sani ba a kauyen Dangaji. Sun kasance suna harbi da kone gidajen wanda kuma ta tilasta mutane gudu don kare rayukansu" in ji daya daga cikin shugabannin al'ummar kauyukan.

"A safiyar ranar Asabar, 13 ga watan Janairu suka kuma tafi wata kauye, Unguwan Gajere inda suka kashe kimanin mutane tara. Daya daga cikin wadanda aka raunana ya mutu a hanyar asibiti".

Shugaban ya ce ‘yan bindigar sun bace kafin sojoji su isa yankunan da wannan harin ta shafa.

Husseini Mukhtar, kakakin hukumar 'yan sandan jihar Kaduna, ya tabbatar da harin, amma ya ce mutane biyar kawai aka kashe, akasarin su ‘yan banga.

Ya ce 'yan sanda da sojoji suna aiki tare a kan yadda za a damke wadanda suka kai harin.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel