Wutan lantarki tayi ajalin wani mutum yayin da yake sare bishiya

Wutan lantarki tayi ajalin wani mutum yayin da yake sare bishiya

- Wani bawan Allah ya gamu da ajalinsa yayin da yake sarar itace a jihar Jigawa

- Ya fara sarar itacen ne alhalin wata reshen itacen na rataye a babban igiyar wutan lantarki

- Hakan yasa wutan tayi masa lahani kuma ya riga mu gidan gaskiya

Wani bawan Allah, Sule Mamman mai shekaru 42 ya hadu da ajalinsa a lokacin da yake sarar wata itace da ke da reshen ta ya jingina da babban igiyar wutan lantarki a Jigawa.

Kakakin rundunar yan sandan jihar, SP Audu Jinjiri ya shaida wa kamfanin dillanci Najeriya (NAN) cewa marigayin Mamman mazaunin kauyen Duhuwa ne da ke karamar hukumar Kiyawa.

Wutan lantarki tayi ajalin wani mutum yayin da yake faskare
Wutan lantarki tayi ajalin wani mutum yayin da yake faskare

"Ranar Juma'a misalin karfe 11 na rana ne muka sami rahoto daga ofishin mu na shuwarin cewa wani mutum mai suna Mamman ya rasa ransa a yayinda yake kokarin sarar itace daga wata bishiya da reshen ta ya taba babban igiyar wutan lantarki.

KU KARANTA: Ka nemi afuwar zagin da kayi mana - Kungiyar Taryyar Afrika ta fadawa Trump

"An sanar da ma'aikatan hukumar wutan lantarki da jami'an yan sanda sannan suka isa inda abin ya faru suka cire gawar sa daga igiyar wutar lantarkin.

"An tafi da gawarsa zuwa Asibitin Kiyawa inda likita ya duba shi kuma ya tabbatar da cewa ya rasu." inji Jinjiri.

A cewarsa, bayan likitan ya tabbatar mutumin ya rasu, an mika gawar sa ga yan uwansa kuma sun yi jana'izan sa kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164