Yadda wata 'yar shekaru 14 ta taimakawa 'yar Chibok wajen kubuta daga Boko Haram

Yadda wata 'yar shekaru 14 ta taimakawa 'yar Chibok wajen kubuta daga Boko Haram

Yarinya 'yar garin Chibok Salomi Pogu wace Boko Haram suka sace tun shekarar 2014 amma ta kubuta daga hannun su mako da ya wuce ta bada labarin yadda wata yarinyar yar shekaru 14 mai suna Jamila yar garin Pulka ta taimaka mata wajen kubutar daga hannun 'yan ta'addan.

'Yan matan biyu Salomi da Jamila, da suke zaune a wani gida na musamman ta gwamnati ta tanadar domin basu tsaro, sun labartawa jaridar Premium Times yadda sukayi jarumta suka gudo daga sansanin yan Boko Haram din.

"Mun zama kawaye ne domin muna makwabtaka a kauyen Ndugne da aka kai mu bayan an sace mu." inji Jamila wadda ke dauke da jaririya yar watanni 16

Bayan nan ne fa suka zama kamar yan uwa duk da cewa akwai banbanci shekaru tsakanin su amma saboda tausayi da taimako da Jamila ke wa Salomi musamman idan tana rashin lafiya, daga baya likitoci sun gano tana da cutar Aneamia.

KU KARANTA: Ya saci babur don ya sayar ya biya sadaki, yayi tsautsayin angwanci a hanya

Jamila wadda tafi sanin yanayin garin tace sunyi kokarin neman hanyar da za su gudu daga baya amma basuyi nasara ba kuma ba'a gano su ba domin duk wanda aka kama yana kokarin guduwa akan zartar masa da hukunci mai tsanin wani lokaci ma kisa akeyi.

"Mun sulale ne cikin dare misalin karfe daya lokacin kowa yana barci har ma da masu gadin mu, mun kuma isa sansanin sojojin ne misalin karfe biyu na daren.

Yan matan sun ce tafiyar da ke tsakanin kauyen na Ndugne da sansanin sojin Najeriya babu nisa sosai amma dai muna ta hadawa ta gudu har muka isa," inji Salomi

Jamila ta cigaba da cewa "Da isar mu sai sojojin suka kar mu kusanto su, suka haska mu ta fitilar kuma suka umurce mu da mu cire tufafin mu domin su tabbatar ba mu dauke da wani abun da zai iya musu lahani, bayan sun ga bamu dauke da komi sai suka ce mu sanya tufafin mu, sannan muka matsa kusa muka fada musu cewa mun gudo ne daga sansanin Boko Haram."

Yan matan sun ce sojojin sunyi matukar muran da suka gano cewa Salomi tana daya daga cikin matan da aka sace a Chibok.

"Kafin wannan lokacin mun taba kokarin guduwa amma bamu gane hanya ba, hakan yasa muka koma kauyen, mun san cewa idan mu zauna ma zamu halaka ko don yunwa ko kuma idan an kawo hari saboda haka kudiri niyyar guduwa" inji yan matan biyu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: