Takardun Boge: Kwalejin ilimi ta dakatar da ma'aikatan ta 500 a jihar Abia
Kimanin ma'aikata 500 ne hukumar makaranta ta dakatar daga aiki a kwalejin ilimi ta jihar Abia dake garin Aba.
Hakan ya faru ne bayan da gwamnatin jihar ta bayar da umarnin bincikar takardun shaidar karatun ma'aikata, shaidar shekaru da kuma binciken ma'aikatan boge.
Jaridar Southern City ta fahimci cewa, a ranar Litinin din da ta gabata ne aka cire sunayen wadanda abin ya shafa daga jerin masu karbar albashi bisa ga bin umarnin hukumar makarantar.
Rahotanni sun bayyana cewa, wasu ma'aikatan kwalejin sun bayar da shekarun karya a yayin daukar su aiki, yayin da wasu suka ketare ka'idojin da suka dace na daukarsu aiki.
A wata ganawar wayar da tarho da manema labarai, kwamishinan ilimi na jihar, farfesa Ikechi Mgbeoji ya bayyana cewa, an cire sunayen wadanda abin ya shafa daga jerin masu karbar albashi bisa ga umarnin gwamnan jihar, Okezie Ikpeazu.
KARANTA KUMA: Ka manta da 2019, magance rikicin makiyaya shine muhimmi a gabanka - Shehu Sani ga Buhari
Yake cewa, an dauki wadanda abin ya shafa aiki ne ba tare da ka'idoji ba, yayin da wasunsu suka bayar da takardun boge.
Kwamishinan ya tuhumi gwamnatin baya da yiwa kwalejin rikon sakainar kashi wajen gudanar da al'amuranta, ya kuma kyautata zato akan gwamnatinsu na daidai al'amura a kwalejin.
LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng