Jami'an tsaro sun yi ram da matsafa 'yan yankan kai a Osun
- Jami'an Hukumar NSCDC da ta 'Yan Sanda sun yi kamen matsafa masu cin kai a Osun
- Wannan lamari ya faru ne gabanin azuhur na ranar Juma'ar da ta gabata
- Jami'an sun samu labarin matsafan ne daga bakin wani dan acaba da ya tsira da ran sa daga hannun su
Rundunar 'Yan Sanda da jami'an Tsaron Al'umma ta Hukumar NSCDC, sun yin kamen matsafa 'yan yankan kai a maboyar su da ke shiyyar Bolurunduro na Ilesa ta Jihar Oshun. Wannan kame ya faru ne gabanin azuhur na ranar Juma'a.
Jami'an sun samu labarin matsafan ne daga bakin wani dan acaba da ya sha da kyar daga hannun matsafan. An kama Kayode Olaniyi mai shekaru 40, da Sunday Ojo mai shekaru 30 sai Kayode Ezekiel mai shekaru 35.
KU KARANTA: Bana goyon bayan ware filayen kiwo na musamman ga makiyaya a Filato - Jonah Jang
Mai magana da yawun NSCDC, Mista Babawale Afolabi, ya tabbatarwa manema labarai da faruwar kamen. Ya kuma yi kira ga al'umma da ta cigaba da bayar da muhimman bayanai don tabbatar da tsaro.
Idan mai karatu bai manta ba, a 2017 ma an yi kamen irin wadannan miyagun mutane a Jihar, wandanda su ka kashe wata dalibar Jami'ar Jihar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng