Dalilin da ya sa na yi watsi da Kristanci na rungumi Musulunci – Inji wata 'yar Nollywood

Dalilin da ya sa na yi watsi da Kristanci na rungumi Musulunci – Inji wata 'yar Nollywood

- Wata ficecciyar dandalin Nollywood ta bayyana dalilin da ya sa ta musulunta

- Wannan shahararriyar ‘yar fim din ta Musulunta ne a shekaru biyar da suka shude

- Anjorin ta ce babu cocin da ta amince su yi wa mahaifiyata jana’iza a lokacin da ta rasu

Wata ficecciyar dandalin Nollywood, wanda aka fi sani da Liz Anjorin, ta bayyana dalilin da ya sa ta yi watsi da Kristanci ta rungumi addinin Musulunci .

‘Yar fim din, wanda aka sani a matsayin Krista, ta Musulunta a shekaru biyar da suka shude, ta bayyana cewa wani mutumi ne sanadiya ta Musulunta.

Legit.ng ta tattaro cewa, Anjorin ta wallafa a shafin sada zumunta ta Instagram dalilin da ya sa ta yanke wannan shawarar.

Dalilin da ya sa na yi watsi da Kristanci na rungumi addinin Musulunci – Inji wata ficecciyar dandalin Nollywood

Ficecciyar dandalin Nollywood, Lik Anjorin

Ta rubuta kamar haka, “”.A lokacin da Allah ya yi wa mahaifiyata rasuwa, fiye da coci goma sun ƙi su yi mata jana’iza

KU KARANTA: Dalilin da ya sa nake bangaren wasan barkwanci — Dangwari

Ta ce duk da matsananciyar da bakin ciki da ta ke tare da shi a wancan lokacin, ta kasa samun cocin da zai taimaka mata.

Ta kara da cewa, "Duk da haka, addinin da ban yi imani da ita ba ta cece ni, suka yi wa gawar mahaifiyata addu’a, suka kuma yi abubuwan da ake bukata, abin da coci ta banu kawai shine filin da muka binne ta".

A cewarta, bayan haka, ta yi alkawarin zuwa Hajji, sa’a nan ta musulunta tun daga lokacin.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel