Sallamar Yusuf Buhari: Shugaba Buhari ya mika godiyarsa ga yan Najeriya
- Rahoto daga mai baiwa shugaba Muhammadu Buhari shawara, Bashir Ahmed ya nuna cewa na sallami Yusuf Buhari daga Asibiti
- Dan shugaba Buharin dai ya samu hadari ne sanadiyar wasa da babur tare da wani abokinsa a cikin garin Abuja
- Shugaba Muhammadu Buhari ya mika sakon godiya ga wadanda suka taimaka da addu'o'insu
A wata jawabi da mai magana da yawun shugaba Buhari, Femi Adesina, ya saki a shafinsa na Facebook yace:
"Shugaba Muhammadu Buhari, uwargidansa, Aisha, da iyalinsa ga baki daya sun mia sakon godiyarsu ga jama'a, na cikin Najeriya da waje bisa ga addu'o'insu wanda Allah ya amsa har aka sallami dansa Yusuf, daga asibiti.
Iyalin suna matukar godiya ga soyayyar da aka nuna musu wanda tun lokacin da Yusuf yayi hadarin babur ranan 26 ga watan Disamba, 2017."
Iyalan suka ce: " Muna godiya ga yan Najeriya daga ko wani bangare da kuma shugabannin kasashen ketare, kungiyoyi, wadanda sukayi addu'a, suka kawo ziyara, suka kawo sakonni, kuma suka tsaya tare da mu lokacin Ibti'la'i."
KU KARANTA: Labari mai dadi: Yusuf Buhari ya samu sauki, an sallamo shi daga Asibiti
An sallami Yusuf daga asibitin Cedarcrest Hospital, Abuja, a yau Juma'a, 12 ga watan Junairu, 2017 bayan ya samu lafiya.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a
http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng