Labari mai dadi: Yusuf Buhari ya samu sauki, an sallamo shi daga Asibiti

Labari mai dadi: Yusuf Buhari ya samu sauki, an sallamo shi daga Asibiti

Da daya tilo ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, Yusuf Buhari na samun sauki sosai biyo bayan jinyar da yayi sakamakon hatsarin babur da ya yi a garin Abuja a ranar, inji rahoton Daily Trust.

Yusuf ya gamu da wannan hatsari ne a ranar 26 ga watan Disamba, sai dai Kaakakin shugabankasa, Femi Adesina ya tabbatar da samuwar sauki ga Yusuf, inda yace babban likitan Asibitin Cedarcrest, Dakta Felix Ogedegbe yace suna gab da sallamar sa.

KU KARANTA: 2040: Addinin Musulunci zai zamto na biyu mafi yawan mabiya a kasar Amurka

Babban likitan yace, a cewar Femi Adesina: “A ranar 26 ga watan Disamba ne aka kwantar da Yusuf Buhari biyo bayan hatsarin babur daya rutsa da shi, bayan da aka farfado da shi, sai muka yi masa tiyata, tun bayan nan ne muka lura yana samun lafiya sosai da sosai, don a yanzu haka muna gab da sallamarsa.

Labari mai dadi: Yusuf Buhari ya samu sauki, ana gab da sallamar shi daga asibiti
Yusuf da Buhari

“Samun saukinsa cikin dan kankanin lokaci manuniya ne ga irin kyawun asibitin mu, don haka muke godiya ga shugaban kasa da Uwargidarsa da suka bamu wannan dama, tare da yarda da aminci da suka nuna mana, hakan zai kara tabbatar da cewa eh za’a yi kulawa da kowani irin cuta ko ciwo a Najeriya.” Inji Likitan.

Ga sanarwar nan:

Labari mai dadi: Yusuf Buhari ya samu sauki, an sallamo shi daga Asibiti
Sanarwar

Daga karshe, shugaban Asibitin ya mika godiyarsa ga ministan lafiya, da kuma sauran likitocin da suka bada gudunmuwa wajen kulawa da Yusuf, sa’annan ya karyata labaran da ake watsawa na cewa wai akwai wani abokin Yusuf da suka yi hatsarin tare, da kuma labarin wai sun kwantar da Aisha Buhari sakamakon hawan jininta daya tashi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng