Shugaban shi'a El-Zakzaky bai mutu ba, yana nan a raye - IMN
- Kungiyar Shi'a tayi karin haske akan halin da shugabanta yake ciki
- Kungiyar ta karyata rahotannin mutuwar shugabanta El-Zakzaky
Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, daurarren shugaban kungiyar shi'a ta IMN, Islamic Movement of Nigeria) yana nan a raye bai mutu ba.
A wata sanarwar ranar Juma'a a shafin dandalin sada zumunta, kungiyar ta shi'a ta yi karin haske sabanin rahotanni da suke yaduwa a fadin kasar nan na cewar shugabanta ya riga mu gidan gaskiya.

Kungiyar ta IMN ta karyata wannan rahoto da cewar shugabanta El-Zakzaky yana nan a raye.
KARANTA KUMA: Gwamna Ambode ya sallami kwamishinoni uku na jihar Legas
Legit.ng da sanadin jaridar The Guardian ta ruwaito a ranar da ta gabata cewa, rashin lafiya ta tsananta akan shugaban na Shi'a, inda cutar hawan yake fama da ita tun shekaru goma da suka gabata ta faskara zuwa bugun zuciya da har ya gaza motsa wasu sassa na jikin sa.
Idan mai karatu bai sha'afa ba, tun a watan Dasumbar shekarar 2015 ne El-Zakzaky ke daure bayan wata arangama da ta afku a tsakanin mambobin kungiyarsa da dakarun soji a garin Zaria.
LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng