Dandalin Kannywood: Maryam Booth ta taka rawa a cikin Fim din Turanci ‘Sons of the Caliphate’

Dandalin Kannywood: Maryam Booth ta taka rawa a cikin Fim din Turanci ‘Sons of the Caliphate’

Shahararriyar jarumar fina finan Kannywood, Maryam Booth ta fito cikin wani sabon shirin Fim na Turanci, mai suna ‘Sons of the Caliphate’, Yayan Sarauta.

Legit.ng ta ruwaito, wannan Fim na nuni ne ga rayuwar wasu matasa yan gida daya dake gogoriyon neman mulki, ramuwar gayya da kuma so da kauna, sune Kalifah, Nuhu da Dikko.

KU KARANTA:

Dandalin Kannywood: Maryam Booth ta taka rawa a cikin Fim din Turanci ‘Sons of the Caliphate’
‘Sons of the Caliphate’

Maryam Booth ta fito ne a matsayin yar maye, wato mai shaye shaye, da nufin fadakarwa a kan illolin shaye shaye ga mai yinsa, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Daga cikin jaruman Kannywood da suka taka muhimmin rawa a cikin wannan Fim, akwai Maryam Booth, Rahama Sadau da kuma Yakubu Muhammed, sa’annan ana nuna wanna shiri ne a duk sati a Ebony Tv.

Dandalin Kannywood: Maryam Booth ta taka rawa a cikin Fim din Turanci ‘Sons of the Caliphate’
Maryam Booth

A wani labarin kuma, afuwar da hukumar tace fina finan Hausa ta yi ma jaruma Rahama Sadau ya bar baya da kura, inda kungiyar yan Fim na Kannywood ta yi watsi da afuwar.

Shugaban kungiyar, Kabiru Maikaba ne ya sanar da haka a ranar Alhamis 11 ga watan Janairu, inda yace har yanzu kungiyarsa bata yafe ma Rahama Sadau ba.

Dandalin Kannywood: Maryam Booth ta taka rawa a cikin Fim din Turanci ‘Sons of the Caliphate’
Maryam Booth

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng