Sallamar Ma'aikata: Kungiyar Kwadago tace Gwamna El-Rufai ba zai ba ta tsoro ba

Sallamar Ma'aikata: Kungiyar Kwadago tace Gwamna El-Rufai ba zai ba ta tsoro ba

- Kungiyar ‘Yan kwadago sun yi zanga-zanga a Garin Kaduna

- Gwamna Nasir El-Rufai ya sallami Ma’aikata 36, 000 daga aiki

- ‘Yan kwadago sun ce Jami’an tsaro ba su hana zu hakkin su ba

Ayuba Waba wanda shi ne Shugaban Kungiyar NLC ta Ma’aikatan kasar yace ba za su fasa abin da su kayi niyya ba domin nuna rashin amannan su da sallamar Ma’aikata sama da 36,000 da Gwamnan na Jihar Kaduna Nasir El-Rufai yayi.

Sallamar Ma'aikata: Kungiyar Kwadago tace Gwamna El-Rufai ba zai ba ta tsoro ba
Kungiyar Kwadago tayi kaca-kaca da Gwamna El-Rufai

Waba yace abin da Gwamnan ya zo da shi rashin imani ne inda yace yanzu Jama’a na neman inda za su ci abinci a Kaduna don haka su ka shirya zanga-zanga domin goyon-bayan mutanen su sai dai Gwamnan ya zuba Jami’an tsaro domin taka masu burki.

KU KARANTA: Gwamnan Kaduna zai kori masu gadi da ‘yan sako daga aiki

Kungiyar kwadago tace a 2012, Malam El-Rufai yana tare da su wajen zanga-zanga amma yanzu ya samu mulki yana kokarin hana Jama’a neman hakkin su. Yanzu haka dai maganar korar Ma’aikatan tana Kotu kuma an nemi Gwamnan ya dakata amma ya ki.

Gwamnan na Kaduna dai ya kori Malamai sama da 21,000 da kuma Ma’aikatan kananan Hukumomi sama da 4,000 da kuma na Jihohi akalla 8,000 da ma wasun su a sauran Ma’aikatu da Makarantu na cikin Jihar Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng