Najeriya za ta fara fitar da shinkafa kasar waje nan da shekarar 2020
- Adadin shinkafar da ake shigowa da ita daga waje ya ragu
- A mulkin Buhari Najeriya na kokarin komawa harkar gona
- Yanzu haka Kasar na daf da noma duk shinkafar da ta ke ci
Bincike ya nuna cewa yawan shinkafar da Kasar Najeriya ke shigowa da ita daga kasashen waje ya ragu matuka daga hawan Shugaban kasa Buhari mulki wanda ya sa ake tunani an kusa daina shigowa da shinkafa cikin Najeriya gaba daya.
Wani rahoto da aka fitar daga shafin Kasar Thailand da ke yawan fitar da shinkafa zuwa kasashen Duniya ya nuna cewa a lokacin Shugaba Jonathan, Najeriya na shigo da sama da metric tonnes Miliyan guda watau 1,239,810 daga waje.
KU KARANTA: Likitocin Najeriya kusan 40,000 ke kasashen waje
Daga hawan Shugaba Buhari dai wannan ya rasu zuwa metric ton 644,131. A shekarar 2016 kuwa abin kara kasa yayi zuwa 58,260. A bara kuwa abin da Najeriya ta shigo da shi na shinkafa daga Kasar waje bai wuce metric ton 23, 197 ba.
Idan aka cigaba da noma shinkafa a gida dai hakan na nufin nan da 2020, Najeriya sai ta noma sama da abin da ta ke bukatar ci har sai ta kai wasu zuwa ketare ga masu bukata. Gwamnatin Buhari dai ta dage wajen ganin an koma noma a Najeriya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng