Dalilin da ya sa nake bangaren wasan barkwanci — Dangwari
Shahararren jarumin nan mai wasan barkwanci a dandalin shirya fina-finan Kannywood, Muhammadu Sani Ibrahim Tsiga wanda aka fi sani da Dangwari ya bayyana dalilan da su ka sa ya rungumin bangaren barkwanci.
A cewar jarumin, marigayi Rabilu Musa (Dan Ibro) shine ya sa masa sha’awar shiga wasan fina-finan Hausa.
Jarumin ya kasance dan asalin jihar Katsina kuma haifafan jihar Kaduna.
A cewarsa marigayi Dan Ibro ne ya karfafa masa gwiwar kwaikwayon gwari domin a cewar sa babu mai wannan baiwar ta kwaikwayon gwarawa a fim. Wato kenan kwaikwayon gwarawa ya zame masa jari.
KU KARANTA KUMA: Gwamna Badaru ya yi wa matar da ta haifi yan hudu sha tara ta arziki (hotuna)
Dangwari ya bayyana cewa ya so ya bar harkar fim a lokacin da labarin rasuwar Dan Ibro ya riske shi amma sai ya ga haka Allah ya tsara don haka ya ci gaba da sana’ar ta sa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng