Yanzu Yanzu: Hawaye na kwaranya yayinda dubban mutane sun halarci taron karrama wadanda harin makiyaya ya cika da su a Benue (hotuna)
Dubban mazauna jihar Benue sun isa babban filin IBB Square dake Makurdi domin halartan taron karrama wadanda harin makiyaya ya cika da su a kwannan nan.
Da dama daga cikin wadanda suka halarci taron na sanye da bakaken kaya domin taya yan uwan wanda abun ya shafa bakin ciki.
Mai kawo wa Legit.ng rahoto dake Makurdi ya gano dogon layi a mashigin wajen taron yayinda dubban mutane ke shiga babban dakin taron.
Daruruwan malamai na wajen domin gudanar da taron tunin.
Haka zalika an tsaurara matakan tsaro a wajen domin su kula da abubuwan da ke kaiwa da komowa.
KU KARANTA KUMA: Ku yi ma Yusuf Buhari addu’a – Gwamna Aregbesola ya roki yan Najeriya
A baya gwamnatin jihar ta kaddamar da yau, Alhamis, 1 ga watan Janairu a matsayin ranar hutu domin mazauna jihar su samu halartan wannan taro.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng